Shugaban Makarantar Firamare ta Maburya na cikin mutane huɗu da aka sake sacewa a sabon harin ’yan bindiga da ya faru a yankin Maburya.**
Wani rahoto da ya iso Maburya Online News ya nuna cewa, an sake sace wasu mutane 4 a wannan makon daga wasu al’ummomi da ke yankin, lamarin da ya ƙara haifar da damuwa game da tabarbarewar tsaro a yankin. Kamar yadda aka ruwaito a baya, an sace kimanin mata da yara 100 a wasu al’ummomin da abin ya shafa. Ko da yake daga baya aka saki mafi yawan waɗanda aka sace, an ruwaito cewa wasu ‘yan mata shida ‘yan ƙanana har yanzu suna hannun masu garkuwa da mutane . Ana zargin cewa ‘yan bindigar na tilasta wa ‘yan matan yin kiwon dabbobi, kuma rahotanni sun ce sun shafe kusan kwanaki goma a cikin zaman talala. A cewar sabon rahoton, mazauna yankin sun nuna damuwa kan abin da suka bayyana a matsayin bayanan yaudara da wasu ‘yan siyasa a yankin ke yaɗawa , inda ake ikirarin cewa an kori ‘yan bindigar daga yankin ko kuma an kama wasu daga cikinsu. Mazauna yankin na fargabar cewa irin waɗannan ikirare na iya sa Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jiha su ɗauka cewa an shawo kan matsalar tsaro, wanda h...